Za a dawo jigilar jiragen kasa daga Lagos zuwa Kano a ranar Juma’a 13 mai zuwa

0 70

Za a dawo jigilar jiragen kasa daga Lagos zuwa Kano a ranar Juma’a 13 mai zuwa.

Manajan yankin arewa na hukumar jiragen kasa, ismail Adibiyi, ya sanar da haka a Zaria lokacin da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na kasa.

Ya ce jirgin kasa zai bar Legas a ranar juma’a da yamma kuma zai isa Kano a safiyar Lahadi.

Ya kara da cewa kamfanin zai gyara tarago 100 don kara karfafa sufurin jiragen kasa cikin watanni biyu masu zuwa.

Ya yi bayanin cewa za a yi amfani da taraguna 21 daga cikin wadanda aka gyara a yankin Arewa, da ya hada da jihoshin Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da kuma Zamfara.

Ya ce jirgin kasa dake jigila daga Kano zuwa Guru har yanzu yana aiki kuma ana cigaba da tsare-tsare da nufin inganta jigila a hanyar ta hanyar dawo da jiragen da aka ajiye saboda annobar corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: