Gwamnatin Tarayya zata jinkirta kaddamar da zagaye na biyu na alurar riga kafin corona

0 73

Gwamnatin Tarayya ta sanar da jinkirta kaddamar da zagaye na biyu na alurar riga kafin corona.

Wannan na kunshe ne a cikin wata gajeriyar sanarwa da daraktan labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Basyy, ya fitar.

Sakataren Gwamnatin Tarayyar, Boss Mustapha, wanda kuma shine shugaban kwamitin corona na shugaban kasa, shine ke jagorantar lamuran corona tun lokacin da aka fara annobar a kasarnna.

Sai dai, gwamnati ta kasa bayar da takamaiman dalilinta na jinkirin, amma ta ce an dauki matakin ne saboda wasu matsaloli da suka kunno kai.

An shirya kaddamar da rigakafin a gobe a cibiyar lafiya ta tarayya dake Jabi a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: