Gwamnatin Tarayya zata baiwa kowacce jiha kudi N5Bn domin tallafawa talakawa a jihohinsu

0 212

Gwamnatin tarayya ta amince ta baiwa kowacce jiha da birnin tarayya Abuja kudi Naira biliyan 5 domin siyo kayan abinci da nufin rabawa ga talakawa a jihohinsu.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno shi ne ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa dake Abuja jim kadan bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa a jiya alhamis.

Wannan ci gaban ya biyo bayan hauhawar farashin kayayyakin abinci, a kasar nan da kuma batun cire tallafin man fetur wanda hakan yayi tasiri wajen tashin kayayyakin.

Baya ga wannan tallafin kudade, gwamna Babagana Zulum ya ce Gwamnatin Tarayya ta kuma saki motocin shinkafa guda biyar ga kowacce gwamnatin jiha 36.

Da yake karin haske, Gwamna Zulum ya ce gwamnonin jihohin za su sayo buhunan shinkafa dubu dari da buhunan masara guda dubu arbai’n da kuma takin zamani.

Ya ce kashi 52 cikin 100 na kudaden an baiwa gwamnatocin jihohi ne a matsayin tallafi yayin da kashi 48 zai kasance a matsayin lamuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: