Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatinsa dangane da cire tallafin man fetur

0 285

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatinsa dangane da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin na da amfani ga kasar nan gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne jiya a Abuja, yayin da yake gabatar da tarihin rayuwar wani dattijon kasar nan, Edwin Clark.

Bola Tinubu, wanda sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya wakilta a wajen taron, ya ce ana kokarin shawo kan illar cire tallafin.

George Akume ya ce yanzu haka gwamnatin tarayya ta aika da takin zamani zuwa Jihohi, an kuma aika tireloli 100 na gero sannan karin wasu na zuwa nan gaba.

Bayan kammala taron da aka yi a fadar shugaban kasa, Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ta amince da kudi Naira biliyan 5 ga kowace jiha da birnin tarayya Abuja a matsayin tallafi ga gwamnatin jihohin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: