Gwamnatin tarayya zata kawar ta’addanci a fadin Najeriya kafin karewar wa’adin shugaban kasa a karshen a 2023 a cewar Femi Adesina

0 81

Mai taiamakawa shugaban kasa Muhammadu buhari a kafafen yada labarai Femi Adesina yace, gwamnatin tarayya zata kawar ta’addanci a fadin kasarnan kafin karewar wa’adin shugaban kasa a karshen a 2023.

Femi Adesina ya bayyana hakan ne a lokacin dayake tattaunawa da gidan telebijin na Channels cikin wani shirin siyasa mai suna Sunday Politics, Inda yace bullo da sabbin hanyoyin yaki da ta’addaci da gwamnatin tarayya ta bullo da su, zasu taimaka wajan samar da tsaro a fadin kasar nan cikin watanni 17 da suke ragewa wannan gwamnatin.

Ya kuma bada misali da yanda aka murkushe yan Tamil Tigers na kasar Sri Lanka, bayan shafe sama da shekara 28, amma a kwana 1 aka kawar da su.

Femi ya kuma jaddada cewa, zasu cafke duk wadanda ke da hannu a wannan rikicin, tare da tabbatar da zaman lafiya kafin buhari ya sauka.

Ya kuma kara da cewa shugaban yanzu haka yana aiki tukuri domin inganta rayuwar yan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: