Gwamnatin tarayya zata mayar da bashin da ake bin Najeriya zuwa tiriliyan 50 zuwa karshen 2023

0 116

Gwamnatin tarayya zata mayar da bashin da ake bin kasar nan zuwa Tirilion 50.22 zuwa karshen 2023, kudaden da suka hada da tiriliyan 28.75 daga cikin gida, sai kuma tiriliyan 21.47 daga kudaden data ciwo daga kasashen ketare.

Wannan na kunshe cikin kudirin shirin hukumar cigaban kasar nan da take son cimmawa daga 2021 zuwa 2025.

Kafin hakan dai hukumar lura da basuka ta kasa a watanni 3 da suka gabata, ta bayyana cewa ana bin kasar nan bashin tiriliyan 38, wannan karin ya biyo bayan yanda gwamnatin ta kara yawan basukan ne a tsakanin watannin Yuli zuwa Satumba na 2021.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu buhari ta shirya ciwo karin bashin tiriliyan 12 daga karshen 2021 zuwa 2023.

Kawo yanzu dai a cewar hukumar lura da basuka ta kasa ta tsara ciwo bashin tiriliyan 348.1 zuwa 2025, yanzu haka basukan da aka ciwo basu wuce kaso 45 cikin 100 na shirin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: