Gwamnonin Arewa Na Bukatar Kudade Masu Kauri Daga Gwamnatin Tarayya Domin dakile Korona

0 86

Kungiyar Gwamnonin Arewa tana bukatar kudade na musamman daga gwamnatin tarayya domin dakile yaduwar COVID-19 a yankin Arewa.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, shine yayi kiran a wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Dr. Makut Machan ya fitar a Jos, bayan ganawar gwamnonin kungiyar ta hanyar faifan bidiyo.

A cewar sanarwar, shugaban yayi zargin cewa an bawa sauran jihoshi wasu kudade na musamman, amma babu wata jiha a Arewa da aka bata, duk da kasancewar an samu bullar cutar a Arewa.

Simon Lalong yace yankin na Arewa yana kokarin fadada hanyoyin tattalin arzikinsa a bangarorin da yake da karfi, domin rage dogaro kacokan da gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: