

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Gwamnatin jihar Jigawa ta dauki alkawarin samar da kayayyakin jin kai ga al’ummar jihar nan, a yanayin da ake ciki na dokar takaita zirga zirga, bayan samun karuwar cutar COVID19 a jihohin da ke makotaka da ita.
Sanarwar hakan ta fito ta bakin gwamnan jihar Jihar nan Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, a yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki a dakin taro na Ahmadu Bello da ke Dutse.

Gwamnan yayi bayanin cewa a yayin da jihohin da ke makotaka da jihar nan da suka hada da Jihar Kano, Bauchi, da kuma Katsina suka samu bullar cutar, gwamnatin jihar nan zata kara tsaurara matakan rufe iyakokin ta.
Kazalika gwamnan ya ce za’a hukunta duk wanda aka kama da karya dokar takaita zirga zirga kamar yanda sabuwar dokar da shugaban kasa muhammadu Buhari ya sanyawa hannu ta tanada.