Gwamnatin Tarayya ta gargadi musulmai a kasarnan da su kauracewa taruwar jama’a wajen bukukuwa da guraren ibada a matsayin wani bangare na hana yaduwar annobar coronavirus, inda tace dole su kasance a raye domin ganin watan Ramadan na bana dama kwanakin da zasu biyo baya.

Jagora na kasa na kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, Dr. Sani Aliyu, shine ya fadi haka a Abuja a taron manema labarai na kwamitin karo na 10.

Sani Aliyu ya bukaci musulmai a fadin kasarnan da su cigaba da kiyaye dokar takaita zirga-zirga tare da sauran matakan da gwamnatin ta dauka lokacin watan Ramadan mai zuwa.

A cewarsa, bawa juna tazara ita ce hanya mafi dacewa, wacce ya kamata a kiyaye sosai a wannan lokacin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: