An samu bullar wata bakuwar cuta a jihar Sokoto – NCDC

0 117

Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 8 da kuma wasu sama da 208 da ake zargin sun kamu da wata bakuwar cuta a jihar Sokoto.

Dr Ibrahim Usman, babban jami’i a cibiyar ne ya bayyana haka a jiya, a wani taron tattaunawa da jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar, inda ya ce lamarin ya faru ne a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na jihar.

Ya kuma ce hukumar ta NCDC da gwamnatin jihar sun dauki matakan gaggawa don shawo kan yaduwar cutar, wadda har yanzu ba a gano ta ba, yayin da aka kai samfurin ta dakin gwaje-gwaje na hukumar don tantancewa.

Ya bayyana cewa cutar ta bayyana da alamun, zazzabi, amai, da rage kiba nan take. A kwanakin baya ne mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Idris Mohammed Gobir, ya shaidawa ministan lafiya, Farfesa Ali Pate, a wata ziyarar ban girma da ya kai masa cewa, wannan bakuwar cuta ta kashe mutane da dama a karamar hukumar Isa ta jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: