Akalla mutane 14 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku da yammacin jiya Lahadi a Kogi

0 123

Akalla mutane 14 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku tsakanin wasu motoci kirar Toyota guda biyu a yammacin jiya Lahadi a jihar Kogi.

Mutane 13 ne suka tsira da rayukansu a hadarin da ya afku a unguwar Aloma da ke karamar hukumar Ofu a jihar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillacin labaran  cewa hatsarin ya hada da wata motar bas kirar Toyota Sienna da ta nufi Abuja daga Fatakwal da wata motar kirar Toyota Hiace da ta nufi kudancin kasa. Mutane 13 da suka hada da direban motar toyota Hiace ne suka rasa rayukan su bayan da wuta ta kone bas din.

Leave a Reply

%d bloggers like this: