Dakarun Sojin Operation Hadin Kai sun gano wata masana’antar Biredi ta ‘yan kungiyar ISWAP

0 73

Dakarun Sojin na Operation Hadin Kai, sun gano wata masana’antar Biredi ta ‘yan ta’adda kungiyar ISWAP a garin Maisani, a karamar hukumar Damboa a jihar Borno.

Wani kwararre mai sharhi akan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya ce majiyoyin leken asiri sun shaida masa cewa, rundunar hadin gwiwa ta bataliya ta 199 ta musamman tare da hadin gwiwar jami’an sa kai ne suka gano masana’antar Biredin a cikin maboyar ‘yan ta’addan a ranar Lahadi.

Zagazola Makama ya wallafa a shafin sa na X, ce wa an lalata masana’antar, yayin da kuma aka kwato kayakin da suka hada da na’urar yin burodi 1 da kuma kayan hada burodi da dama. Makama ya ci gaba da bayyana cewa, aikin kakkabe yan ta’addan na tsawon mako guda, ya yi nuni da yadda sojoji suka yi kaca-kaca da maboyar yan ta’addan a yankunan  Talala, Ajigin, Dusula, Abulam, Gorgi, a yankin Timbuktu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: