An Dakatar Da Haska Kwana Casa’in Da Gidan Badamasi

0 273

A yau talata Hukumar Tace Fina Finai ta jihar Kano ta fitar da sanarwa wacce shugaban Hukumar Malam Ismael Naabba Afakallah ya sanyawa hannu, wacce a cikinta aka nemi da Gidan Television na Arewa24 dasu dakatar da haska Shirin Kwana Chasa’in da Gidan Badamasi har sai sun kaiwa Hukumar ta tace kamar yadda dokokin hukumar suke.

Censorship Board Law 2001 yayi nuni da cewa kowanne irin shirin film na Hausa da zaa haska wanda Kanawa zasu kalla, ka’ida ne hukumar tace fina finai ta tantanceshi kafin al’umma su kalla, haka nan a cikin dokokin hukumar na Section 100 (2) sun bayyana cewa rike mace a cikin film din Hausa haramun ne.

Hukumar ta baiwa Gidan Television na Arewa24 waadin awa Arba’in da takwas dasu dakatar da haska shirin Kwana Chasa’in da gidan Badamasi nan take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: