Daga Yanzu an Cire Tallafin Man Fetir Gaba Daya A Nijeriya

0 152

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC, Mele Kyari, yace zamanin tallafin man fetur a Najeriya yazo karshe.

Da yake jawabi ga gidan talabijin na AIT jiya Litinin, Mele Kyari yace babu sauran tallafin mai a Najeriya, an dena shi kwata-kwata.

Mele Kyari ya bayyana kamfanin na NNPC a matsayin mai gudanar da aikinsa bisa gaskiya, inda yace kamfanin zai iya zama shine kadai kamfani a duniya da yake wallafa rahoton kudadensa da ayyukansa a kowane wata.

Shugaban na NNPC ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya wadatuwar man tare da rarraba shi zuwa ko’ina a fadin kasarnan, inda yace duk da annobar coronavirus, kamfanin yana da lita biliyan 2 da miliyan 600 na man fetur a ajiye, wanda zai wadaci bukatar man kasarnan har nan da watanni 2 masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: