’Yan Najeriya Ku Yafe Ni Kan Karanci Wuta -Ministan Lantarki

0 308

Ministan Lantarki a Najeriya, Injiniya Saleh Mamman, ya nemi afuwar ’yan Najeriya kan rashin samun wadatacciyar wuta da suke fuskanta a yanzu.

Ministan ya nemi afuwar ne cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter da misalin karfe 11.23 na safiyar Alhamis.

A yayin da yake bayar da tabbacin cewa komai zai gyaru na ba da jimawa ba, Ministan ya alakanta karancin hasken lantarkin da wasu matsaloli da ake fuskanta a cibiyoyin samar da wutar guda takwas na kasar.

Cibiyoyin sun hada Sapele, Afam, Olonrunsogo, Omotosho, Ibom, Egbin, Alaoji da Ihoybor.

Injiniya Mamman ya kuma ce matsalar na da nasaba ne da rufe cibiyar wuta ta Jebba domin aiwatar da wasu gyare-gyare da aka saba duk shekara.

Kazalika, Ministan ya bayyana wasu cibiyoyi bakwai da suka hada Geregu, Sapele, Omotosho, Gbarain, Omuku, Paras da Alaoji wanda a cewarsa suna fama da karancin iskar gas.

Ya kara da cewa, akwai gyare-gyare da tashar samar da wuta daga ruwa ta Shiroro ke bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: