Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce sojojin Eritrea sun kashe mutane 3 tare da jikkata akalla wasu 19 a yayin wani harin babu gaira ba dalili kan fararen hula a kasar Habasha.

Bayan shafe tsawon watanni mahukunta na karyata zargin take hakkin dan adam, a watan da ya gabata Firaministan Habasha ya amince cewa sojojin Eritrea na dafawa dakarun kasarsa a yankin Tigray.

Wadanda suka shaida lamarin sun fadawa Amnesty International cewa sojojin na Eritrea na wucewa ne ta garin Adwa a ranar Litinin, yayin da suka bude wuta a kusa da tashar motar garin.

Wasu rahotanni sun ce sun yi ta ihu ga mutane don su kawar da ababen hawansu daga kan hanya.

Mahukunta a Asmara babban birnin kasar ba su mayar da martani kan zargin ba.

A watan jiya ne Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce Eritrea ta amince ta janye dakarunta daga kasar, sai dai har zuwa yanzu ba a sanya rana ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: