Wata guguwa mai karfi ta lalata gidaje sama da 200 da kayayyaki na miliyoyin nairori a garuruwan Wukari da Donga a jihar Taraba a jiya.

Mazauna garuruwan biyu, Idi Muhammed da John Dauda, sun shaidawa manema labarai a wata ganawa daban-daban cewa guguwar tazo kafin wani mamakon ruwan sama wanda ya dauki kusan awanni 2.

Idi Muhammed yace guguwar ta lalata gidaje da dama da wata coci da ababen hawa a garin Wukari.

Yace a saboda haka, mutane dayawa sun rasa gidajensu, amma babu rahoton wanda ya rasa ransa.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun yi kira ga gwamnatin jihar Taraba da ta agaza musu da kwanon rufi domin gyara gidajensu.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Adi Daniel Grace, yayi kira ga hukumar agajin gaggawa ta jihar da ta samar da kayan tallafi ga wadanda iftila’in ya rutsa da su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: