Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rajistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.

Ministan Sadarwa da tattalin Arziki na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita.

Ministan ya ce za’a cigaba da rajistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatarsa ta samar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: