Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta kama wasu matasa da tsakar rana suna cin abinci a wannan lokaci na Azumin watan Ramadana.

Hukumar ta cafke maza uku da mata takwas suna dibar abinci wanda ya nuna ba sa yin azumi.

A cewar shugaban Hukumar, Dokta Aliyu Musa Kibiya, suna binciken wadanda aka kama domin jin dalilansu na rashin azumtar watan Ramadana kasancewarsa wajibi ga duk wani baligi mai cikakkiyar lafiya.

Sai dai Dokta Kibiya ya ce suna da masaniya a kan uzuri da aka yi wa mata masu al’ada ko tsofaffi da ba za su iya jure yunwa ko kishirwa ba.

Kamar kowace shekara, hukumar takan gudanar da irin wannan kame a cikin birni da Kananan Hukumomin Kano kamar yadda manema labarai na BBC Hausa suka ruwaito.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: