Ranar Juma’a Babu Aiki A Nijeriya

0 102

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a mai zuwa 10 ga watan Afrilu, da Litinin, 13 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun Easter na bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya ayyana hutun a madadin gwamantin tarayya, cikin wata sanarwa da babar sakatariyar ma’aikatar, Georgina Ehuria, ta fitar a Abuja.

Mista Aregbesola ya bukaci kiristoci a kasar nan da su yi koyi da kyawawan dabi’un Yesu Almasihu, wadanda daga cikinsu akwai hakuri, kaunar jama’a, san zaman lafiya da tausayi.

Yayi kira ga kiristoci da su yi amfani da ranakun bikin Easter na bana domin gabatar da addu’o’i ga Najeriya dama duniya baki daya a wannan lokacin da ake ciki, na fama da annobar coronavirus a fadin duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: