Matakan da Gwamnatin Jigawa ke Dauka don Dakile Yaduwar Korona

0 211

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana shirinta na fadada cibiyar killace masu cutar covid 19, ta yadda zata dauki gadaje 300, sabanin guda 20 da take dashi a yanzu haka.

Shugaban rundunar kar ta kwana kan yaki da cutar, kuma kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abba Zakari, shine ya bayyan hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.

Yace gwamnati na duba yuwuwar amfani da otal din 3star dake Dutse, da kuma sansanin masu hidimtawa kasa, da sauran wurare daban daban daga shiyyoyi ukun santoriyar jihar’

Dr. Zakar yace sakamakon gwajin mutum 5 da akayi na cutar Covid-19, daga kananan hukumomin Kafin Hausa, Jahun, Birniwa da Kaugama, ya nuna cewa basa dauke da cutar.

Ya kuma ce akwai karin gwaji 2 da za’a aika domin tabbatarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: