Cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 150 tsakanin Janairu zuwa Maris ɗin 2024

0 43

Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka NCDC a Najeriya ta tabbatar cewa cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 150 tsakanin Janairu zuwa Maris ɗin 2024.

NCDC wadda ta fitar da alƙaluman cikin wani rahoto da ta saki ranar Alhamis, ta ce mace-macen sun faru ne a ƙananan hukumomi 125 daga jihohi 27 a Najeriya.

A jumulla NCDC tace daga mako na ɗaya zuwa na 13 na wannan shekarar, mutanen da suka mutu sanadin kamuwa da cutar lassa sun kai kashi 18.6 cikin 100 wanda ya ɗara adadin da aka samu a irin wannan lokaci a bara wanda adadin yake kashi 17.5 cikin 100.

Hukumar ta ce an tabbatar mutum 806 sun kamu da zazzaɓin lassa cikin mutum 5,295 da ake zargi cutar ta harbe su a jihohin da lamarin ya shafa.

A cewar NCDC, kashi 62 cikin 100 an bayar da rahotonsu ne daga Bauchi da Edo da Ondo da kuma Filato. Sai dai ta ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a mako na 13 na wannan shekarar ya ragu zuwa 15 daga 25 da aka bayar da rahoton a makon da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: