Wata Sabuwa: Yan Tijjaniyya Sun Dage Taron Maulidi Saboda Korona

0 88

Darikar Tijjaniya ta dage Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na kasa da ta saba gabatarwa duk shekara har sai lokacin da hali ya yi saboda matsalar cutar Korona Virus.

Jagoran Darikar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya bayyana hakan. Ya ce an dau wannan matakine saboda shawarwarin masana harkar lafiya suka bayar da nufin dakile yaduwar cutar ta Korona Virus.

An tsara gudanar da taron na bana ne a biranen Abuja da Sokoto ranar 21 ga wannan watan. Taron ya hada al’umma daga dukkanin bangarori na Najeriya da ma kasashen duniya.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, manyan malaman Musulunci da mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya da suka hada da Senegal, Ingila, Morocco, Burtaniya da kuma kasar Amurka da ma wani yankin na Nahiyar Asiya, sun bayar da shawarar dakatar da taron saboda yanayin yawan al’ummar da taron yake hadawa.

Shehin Malamin ya shawarci al’umma da su dukufa wajen addua’a tare da karanta Hasbunallahu wa Ni’imal Wakilu kafa 450 duk rana don kawo karshen cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: