Yadda Ta Kaya Tsakanin Gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU

0 273

Gwamnatin tarayya da shugabanin Kungiyar Hadinkan Malaman Jami’o’i ta ASUU ba su cimma wata yarjejjeniyaba jiya kan yajin aikin makonni 2 na gargadin da kunigyar take gabatarwa.

Bangarorin biyu, sun zauna jiya Talata 17 ga watan Maris domin samo bakin matsalolin da Kungiyar ta gabatar ga Gwamnati.

Ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa a zaman da aka debe tsawon wuni guda ana gabatarwa, Gwamnati ta gabatar da tsare-tsaren yanda ‘yan Kungiyar za su kasance a cikin tsarin biyan albashi na IPPIS.

Dukkan bangarorin biyu basu bayyanawa manema labarai irin tsare-tsaren da aka gabatarba.

Ministan Kwadagon ya kara da cewa, abubuwan da aka sa agaba wajen dubawa sun hada da kudaden gudanar da jami’o’i, da kuma inganta jami’o’in gwamnati da ma matsalar albashi da ta alawuns alawuns.

Yajin aikin makonni biyun da Kungiyar ASUU ta keyi, zai zo karshe ne a ranar Litinin ta mako mai zuwa.

Kungiyar ASSUn ta bayyana cewa ta shiga yajin aikin ne saboda matsalar rashin biyan albashi ga mambobinta da ba su shiga tsarin gwamnati na IPPIS ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: