Yajin Aiki: ASSU Da Gwamnati Zasu Zauna Don Tattaunawa

0 84

Kungiyar malaman jami’o’in kasarnan, ASUU, tare da gwamnatin tarayya zasu zauna a yau Talata, domin shawo kan yajin aikin gargadi da malaman ke yi a halin yanzu.

An tabbatar da zaman tattaunawar daga bakin wasu manyan jami’an kungiyar jiya Litinin da dad dare.

Wani jami’i yace zaman tattaunawar tare da gwamnatin tarayya zai gudana da misalin karfe 3 na yamma.

Sannan, daga wata majiya, an ce gwamnatin tarayya bata biya albashi ga malaman ba, sai dai ta biya wadanda suka shiga tsarin biyan albashi na IPPIS.

Zaman tattaunawar shine zai zama na biyu, tun bayan da kungiyar ta fara yajin aikin gargadi a makon da ya gabata.

Kungiyar tana kuma adawa da rashin kudade, da karuwar yawaitar jami’o’in jihoshi da kuma rashin cika alkawarukan da aka dauka a baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: