Gwamnonin Arewa Su Zauna da Tinubu Don Kyautata Dangantaka da Nijar – Dasuki

0 114

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tambuwal da Kebbe, Abdulsamad Ibrahim Dasuki, ya buƙaci gwamnonin Arewa su gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin tattauna yadda za a inganta dangantaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Dasuki, ya ce kyautata dangantakar ƙasashen biyu na da muhimmanci saboda matsalar tsaro da ke ƙara ƙamari a yankunan da ke da iyaka da Nijar.

Ya bayyana hakan ne a hedikwatar jam’iyyar ADC da ke Sakkwato bayan shugabannin Ƙananan Hukumomin da yake wakilta sun karrama shi bisa matsayinsa na Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai.

Ya ce matsalar rashin tsaro ta yi ƙamari musamman a yankunan Gabas da Kudancin Jihar Sakkwato, ciki har da Fakai, Sabon Birni da sauran wurare.

“Gaskiya matsalar tsaro ta yi yawa. Gwamnatin Tarayya da ta jiha sun kasa kawo mafita, kuma har yanzu ba mu ga wani mataki da aka ɗauka ba,” in ji shi.

Dasuki ya kuma shawarci Gwamnan Sakkwato ya gana da Shugaba Tinubu domin a bai wa jihar damar kafa rundunar masu tsaron daji kamar yadda aka yi wa jihohin Oyo da Katsina, saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Dangane da batun ƙirƙirar ’yan sandan jihohi, ya ce sun amince da ƙudirin samar da su a Majalisar Wakilai saboda muhimmancin tsaro da kuma kauce wa siyasantar da lamarin.

Da yake magana kan siyasa, Dasuki ya bayyana cewa yana da yaƙini jam’iyyar ADC za ta yi nasara a zaɓen 2027, amma ya ce akwai buƙatar wayar da kan jama’a game da illar sake zaɓen APC.

Haka kuma, ya ce mafi ƙarancin albashi a Jihar Sakkwato ya kamata ya kai Naira dubu 150 domin gwamnati za ta iya biyan kuɗin.

Leave a Reply