Gwamnonin jam’iyyar PDP suna gudanar da taron ganawar sirri

0 56

Gwamnoni 12 na Jam’iyar PDP ciki harda Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu, suna gudanar da taron ganawar sirri a Gidan Gwamnatin Jihar Rivers da ke birnin Fatakol.

Kimanin Gwamnoni 13 ne suka halarci zaman sai dai kuma Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, bai halarci zaman ba, har zuwa wannan lokaci.

Shugaban Jam’iyar PDP na Kasa Iyorchia Ayu, ya halarci zaman a Makare, bayan an jima da fara gudanar da taron.

Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da na Jihar Benue Samuel Ortom, Bauchi State Governor Bala Mohammed; Sokoto State Governor Aminu Tambuwal; Oyo State Governor Seyi Makinde; Enugu State Governor Ifeanyi Ugwuanyi; Delta State Governor Ifeanyi Okowa.

Sauran mahalarta taron sun hada da Gwamnonin Jihohin Akwa Ibom State Governor Udom Emmanuel; Abia State Governor Okezie Ikpeazu; Adamawa State Governor Ahmadu Fintiri.

An bada rahotan cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Mahdi Aliyu na daga cikin Mahalarta taron.

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, shine ya shirya zaman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: