‘Karancin malamai a Makarantun Polytechnics na cigaba da dakushe kokarin kwalejojin wajen samar da Ilimi mai inganci’

0 59

Hukumar Lura da Ilimin Kwalegin Fasaha ta Kasa ta ce Karancin Malamai a Makarantun Polytechnics na cigaba da Dakushe kokarin Kwalejojin wajen samar da Ilimin Fasaha a kasar nan.

Hukumar ta ce Kwalejojin Fasaha Mallakin Gwamnatin tarayya na fuskantar mutuwa, biyo bayan karancin Malamai, kuma gwamnati taki daukar sabbi domin cike gibin da ake dashi.

Wata Majiya a hukumar ta fadawa Manema Labarai cewa wasu daga cikin Kwalejojin Polytechnic din sun fadi tantancewar da hukumar take yi musu, saboda karancin Malaman da ake bukata.

Shugaban Hukumar na Kasa Farfesa Idris Bugaje, da Kungiyar Shugabannin Makarantun Fasahar sun rubutawa Ministan Ilimin na Kasa Malam Adamu-Adamu da Shugabar Ma’aikatan Gwamnati kan bukatar daukan sabbin Malaman amma abin ya ci tura.

Cikin Wata takarda da Farfesa Bugaje ya aikewa da Ministan Ilimin a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa mafiya akasarin Kwalejojin Fasaha na tarayya zasu rasa shaidar Kwarewar da suke da ita matukar ba’a magance matsalar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: