Kungiyar Gwamnonin jam’iyar APC sun nanata cewa za su gudanar da babban taron kasa a watan Fabreru

0 23

Kungiyar Gwamnonin da aka zaba karkashin tutar Jam’iyar APC sun sake nanata cewa Jam’iyar zata gudanar da babban taron ta na Kasa a watan Fabreru na wannan shekara.

A watan Nuwambar shekarar bara ne, Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, da Gwamna Badaru Abubakar sun bayyana cewa shugaban Buhari ya amince a gudanar da babban taron Jam’iyar a watan Fabreru.

Manema Labarai sun rawaito cewa Kwamatin Rikon Kwarya na Jam’iyar, karkashin Jagorancin Gwamna Mai Mala Buni zai gana a gobe Talata.

Da suke tattaunawa da Manema Labarai bayan kammala zaman na su a jiya Gwamnonin Jihohin Kebbi da Jigawa sun nanata cewa taron Jam’iyar zai gudana ne a watan Fabreru, inda suka kara da cewa Kwamatin Mai Mala Buni zai sanya ranar gudanarwa.

Kazalika, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Jam’iyar APC sun amince a gudanar da taron a watan Fabreru na wannan shekara kamar yadda aka tsara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: