Hadakar gonaki da kasuwancin kifi zai samarwa mutum 4000 ayyukan yi a jihar Borno

0 82

Gwamnatin tarayya tace hadakar gonaki da kasuwancin kifi a jihar Borno zai samarwa yan asalin jihar mutane 4,000 ayyukan yi, wadanda suke dawo daga sansanin yan gudun hijira.

A cewar gwamnatin tarayya kadada 100 zata samarwa mazauna yan kunan karkara dubu 1,500 ayyukan yi, kuma mutane 2,500 zasu samu ayyukan yi daga wuraren kiwon kifi 2.500.

Babban sakataren hukumar kula da cigaban filayen noma na kasa Paul Ikonne, shine ya bayyana hakan yayinda yake rangadin ayyukan da hukumar ta gudanar a jihar borno.

Sakataren ya ce gonakin nomar da aka samar a karamar hukumar Jere, zai fara aiki kafin karshen wannan shekarar da muke ciki.

Ya kuma kara da cewa kayan aikin da aka samar zai baiwa yan gudun hijira damar dawowa muhallan su tare da cigaba da aikin noma, tare da kyakkawan muhalli don gudanar da aikin noma.

Kazalika yace manufar gwamnatin tarayya shine ta tabbatar wadanda suka bar muhallan su na asali sun dawo, da kara habaka fannin noma da kuma sanya matasa a harkar noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: