“Kudurin halasta amfani da tabar wiwi bazai yi nasara ba a gaban majalissar dokoki ta kasa”, Buba Marwa

0 82

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi Brig. Gen. Buba Marwa, yace kudurin halasta amfani da tabar wiwi bazai yi nasara ba a gaban majalissar dokoki ta kasa.

Buba Marwan yayi gargajin cewa duk dan majalissar da ya goyi bayan kudurin halasta dokar amfani da tabar wiwi bazai koma kujerar sa ba.

Shugaban hukumar ya bayyana hakane a jiya Juma’a, yayinda yake ganawa da Wakilin majalissar dokokin ta kasa bayan sun kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kazalika ya bayyana cewa shan tabar wiwi yayi sanadin rasa rayuka da dama akasar nan, don haka baza a halasta amfani da it aba domin samun wata riba.

Ya kuma kara da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayar da tabbacin illar da tabar ta ke yiwa kwakwalwa, bugu da kari Nigeria na da yawan mashaya wiwi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: