An sanya dokar kulle a Guinea bayan hamɓarar da mai tazarce Alpha Conde

0 682

Kamar yadda jaridar BBCHausa ta wallafa, “sabuwar gwamnatin soji a Guinea ta sanya dokar hana fita har sai abin da hali ya yi. A ranar Lahadi ne sojojin suka kwace mulki suka kuma kama Shugaba Alpha Conde.

A sanarwar da suka fitar sun ce shugaban na cikin koshin lafiya, kuma sun rusa gwamnati tare da nada sojoji a matsayin gwamnoni.

Bugu da kari sun kira ministoci wani taron gaggawa a yau Litinin, inda suka ce duk ministan da bai halarci taron ba sunansa dan tawaye.

A cewar Mr Doumbouya, sun yi juyin mulkin ne domin kawo karshe cin hanci a Guinea.

Leave a Reply