Gwamnatin tarayya ta amince da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan Hukumar NIMC

0 79

Gwamnatin tarayya ta amince da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan Hukumar Shaidar Zama dan Kasa, watanni bakwai bayan ma’aikatan sun yi zanga-zanga kan rashin isassun kudade.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, ya sanar da hakan a Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hukumar karkashin ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki a watan Oktoban bara.

A ranar 7 ga watan Janairu, ma’aikatan hukumar suka fara yajin aiki saboda rashin walwalar ma’aikata da bazaranar corona, yayin rajista Lambar Shaidar Zama dan Kasa.

Pantami ya ce sabon tsarin aiki da sikelin albashi ya ninka jumillar kudaden albashin ma’aikatan hukumar sau 3.

Mukaddashin shugaban kwamitin gudanarwa na Hukumar Hukumar Shaidar Zama dan Kasa, Bello Gwandu, ya ce tun shekarar 2010 ake kokarin samun nasarar karin albashin ma’aikatan hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: