Mutum 19 ne ake fargabar sun mutu yayin da aka rasa mutane da dama a wani sabon harin ‘yan bindiga a jihar Neja

0 105

Akalla mutane 19 ne ake fargabar sun mutu yayin da aka rasa mutane da dama a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a Magami, wani kauye a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

‘Yan bindiga hudu na daga cikin wadanda aka ruwaito sun rasa rayukansu a harin.

An rawaito cewa harin ramuwar gayya ce ga kisan da aka yiwa ‘yan fashin daji a baya-bayannan, yayin arangama da mafarautan yankin da ‘yan kato da gora.

Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindiga sun kaddamar da harin ne bayan mafarauta da ‘yan kato da gora na yankin sun koma sansaninsu da ke Galadima Kogo.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta iya tabbatar da harin ba yayin da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya gaza amsa kiran wayarsa.

Bai kuma amsa sakon tes da wakilinmu ya aika masa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: