Hanyoyin Aikewa Da Kayan Abinci Zuwa Jihohi Ba Zasu Samu Matsala Ba – Nanono

0 78

Gwamnatin Tarayya tace ta fara shirin tabbatar da cewa ana samun saukin safarar amfanin gona tsakanin jihoshi.

Ministan aikin gona da raya karkara, Sabo Nanono, ya kaddamar da kwamitin fasaha na magance cutar corona, domin saukaka jigilar amfanin gona a fadin kasarnan.

A wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, Sabo Nanono yace kwamitin zai assasa jigilar amfanin gona ba tare da shamaki ba, kuma a kyauta, a fadin kasarnan, lokacin dokar kulle da kuma lokacin damunar bana, domin kaucewa karancin abinci.

Wannan cigaban yazo ne bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Sabo Nanono da sauran ministoci da su tabbatar da cewa dokar kullen bata shafi lokacin damuna ba.

Da yake mayar da martani a madadin kwamitin, mataimakin sufeto janar na ‘yansanda, Austin Agbonlahor, yayi alkawarin jajircewar kwamitin wajen aikin da aka saka a gaba, tare da alkawarin cimma burin da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: