Hedkwatar tsaro ta fusata kan yadda wasu yan siyasa ke sanya kakin sojoji da kayan ado na yakin neman zabe

0 77

Hedkwatar tsaro ta fusata kan yadda wasu ‘yan siyasa ke sanya kakin sojoji da kayan ado na yakin neman zabe.

Hedkwatar ta ce ana nuna hotunan yakin neman zabe na wasu gwamnoni sanye da kakin sojoji a wuraren da dama jihohinsu.

Hedikwatar tsaro ta lura cewa ba bisa ka’ida ba ne kuma cin zarafi na damar barin fararen hula su sanya kakin soji a lokacin atisayen soja.

Matakin na hakumar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Air Commodore Wap Maigida.

Wani Bangaren sanarwar ya ce ya zama dole a sake bayyana cewa rundunar sojin Najeriya a matsayinta na kwararrun cibiya, ta ci gaba da kasancewa a siyasance, don haka ba za ta so a jawo ta cikin kowace irin salon siyasa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: