Rundunar yan sandan jihar Jigawa sun kama masu garkuwa da mutane a jihar Jigawa

0 86

Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta kama masu Garkuwa da mutane a jihar Jigawa, ciki harda wasu mutum biyu da ake zargi da aikata Garkuwa a jihar a baya-bayan nan.

Kakakir rundunar na jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kame mutanen cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

An bayar da rahotan cewa wasu mahara da yan fashi dauke da muggan makamai a ranar 12 ga watan desembar bara, sun kai hari garin Bosuwa inda suka yi Garkuwa da wani dattijo mai shekara 70 a duniya mai suna Alhaji Ali Umar da wata budurwa Zainab Isah mai shekara 23 zuwa wani waje da ba’a san ko inane ba.

Kakakin rundunar yace bayan samun rahotanni tawagar jamian yan sanda daga chaji ofishin Garki sun kama wasu da ake zargi.

Wadanda ake zargin sun hada da Rabiu Audu mai shekara 35, dakuma Alhaji Isah Muhammad mai shekaru 43 dukaninsu a sansaninsu dake kauyen Dandagare a Karamar hukumar Garki.

ASP lawan Shiisu yace kwamashinan yan sandan jihar Jigawa cp AS Tafida ya bada umarnin mayar da karar zuwa ofishin binciken kwakkwafi a Dutse domin fadada bimcike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: