

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin wata tattaunawa da aka watsa a jiya yayi watsi da alkaluman tabarbarewar tattalin arziki a karkashin mulkinsa inda yake kira ga ‘yan Najeriya su rungumi aikin gona domin magance tulin matsalolin tattalin arzikin kasarnan.
A tattaunawar, wacce ma’aikatan gidan talabijin na Channels, Seun Okinbaloye da Maupe Ogun-Yusuf suka gabatar, shugaban kasar ya musanta wasu daga cikin alkaluman da masu gabatarwar suka lissafa dake nuna tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare tun bayan hawansa mulki a shekarar 2015.
A tattaunawar, Okinbaloye ya kwatanta alkaluman tattalin arziki tsakanin shekarar 2015 da 2021, inda yayi bayanin yadda alkaluman suka damu ‘yan Najeriya dangane da mummunan halin tattalin arziki.
Amma shugaba Buhari ya mayar da martani ta hanyar watsi da alkaluman da ‘yan jaridar suka lissafa, amma ya kasa kare kansa. Daga baya ya sake maimata ikirarinsa na cewa dole ‘yan Najeriya su koma gona kafin a iya gyara tattalin arziki.
Shugaban kasar yayi ikirarin cewa kashi 2 da rabi cikin 100 ne kadai na kasar noma a kasarnan ake iya nomawa.