shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, yace dabara ta karewa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yadda zai ciyar da kasarnan.

Iyorchia Ayu ya fadi haka a matsayin martani akan matsayar shugaban kasa kan wasu batutuwa a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channles a jiya.

Daga cikin batutuwan da shugaba Buhari yayi magana akai sun hada da rikicin makiyaya da manoma da neman kirkirar yansandan jihoshi da takaddamar dokar zaben da aka gyara da kalubalen tsaro da kuma zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Da yake mayar da martani akan sabunta matsayar shugaba Buhari akan rikicin makiyaya da manoma, Iyorchia Ayu ya zargi shugaban kasar da nuna halin ko in kula akan zubar da jinin da kudirin ke haifarwa.

Yace shugaban kasar ya tabbatar da abinda ‘yan adawa suka yi ta nanatawa na cewa dabara ta karewa gwamnati mai ci akan yadda za ta ciyar da kasarnan gaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: