

- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wakilai uku na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP daga karamar hukumar Mariga ta jihar Neja - May 26, 2022
- Dalilan da yasa wasu ‘yan takarar gwamna 2 na jam’iyyar APC suka yi watsi da zaman ganawar da gwamna Badaru ya kira domin a samar da dan takarar daya tal - May 26, 2022
- Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari ya garzaya wata babbar kotun tarayya domin neman belinsa - May 26, 2022
Dakarun operation hadin kai sun kashe mayakan Boko Haram da na ISWAP 950 tsakanin ranar 20 ga watan Mayun bara zuwa 6 ga watan Janairun da muke ciki, a cewa helkwatar tsaro.
Mukaddashin daraktan yada labaran tsaro, Bernand Onyeuko, ya sanar da haka lokacin da yake tilawar cigaban da aka samu yau a Abuja.
Onyeuko yace dakarun sun dakile manyan kwamandoji da jagororin kungiyoyin mayakan cikin watannin.
Yace mayaka dubu 24 da 59 da iyalansu da suka hada da manyan maza dubu 5 da 326 da manyan mata dubu 7 da 550 da yara dubu 11 da 183 kawo yanzu sun mika wuya ga sojoji.
Daraktan yace dukkan wadanda suka mika wuya an tantancesu tare da mika su ga hukumomin da suka kamata domin matakan gaba.
Onyeuko ya kara sanar da cewa sojoji sun kama mayaka 79 yayin da aka ceto fararen hula 113 cikin watannin.