Gwamnatin Jihar Jigawa tace ta kashe kudi sama da naira miliyan 160 a yakin da take yi da bahaya a waje a shekarar da ta gabata.

Manajin darakta na hukumar samar da ruwan sha a karkara da tsaftar muhalli (RUWASA) Labaran Adamu, ne ya bayyana hakan.

A cikin wata fira da aka yi da shi a jiya, Labaran Adamu yace an kashe kudaden wajen wayar da kan mutane akan illar bahaya a waje a jihar.

A cewarsa, an kashe kudaden wajen ilimintar da mutane domin sauyin dabi’a wajen amfani da bandaki.

Labaran Adamu yana magana ne akan bukatar gwamnati na ganin jihar Jigawa ta zama ta farko da zata kasance an dena bahaya a waje a fadin kasarnan.

Ya kuma sanar da cewa gwamnatin jihar na aiki akan wani kudiri da zai tursasa kiyayewa da dokar haramta bahaya a waje.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: