Hukumar EFCC ta gurfanar da ‘yan kasashen waje 146 bisa laifin damfara ta yanar gizo

0 339

Hukumar EFCC ta ce ta gurfanar da ‘yan kasashen waje 146 bisa laifin damfara ta yanar gizo da yawancinsu ke amfani da takardun ‘yan Najeriya.

Shugaban EFCC Ola Olukoyede ya bayyana hakan a wani taron kariya daga hare-haren yanar gizo da aka gudanar a Abuja.

Ya ce wadanda aka yanke wa hukunci za a mayar da su kasashensu bayan sun kammala zaman gidan yari.

EFCC na kuma shirin kaddamar da cibiyar sa ido da za ta gano hare-haren yanar gizo cikin kasa da awa daya.

Olukoyede ya bukaci karin hadin kai tsakanin bankuna, hukumomi da kasashen duniya don dakile barnar intanet.

Leave a Reply