Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta tabbatar da kama gungun wasu matasa maza da mata su 78 suna tsaka da aikata masha’a

0 60

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta tabbatar da kama gungun wasu matasa maza da mata su 78 suna tsaka da aikata masha’a a wani gidan casu mai suna ‘White House’ a unguwar Nassarawa GRA.

Shugaban Hukumar, Harun Ibn Sina, ya shaida wa manema cewa sun kama matasan ne bisa zargin aikata fasadi da kuma yin shiga ta bayyana tsiraici, amma ya karyata rade-radin da ke yawo cewan an kama matasan ne suna hada auren jinsi a tsakaninsu.

Wadanda ake zargin sun kunshi da maza da mata.

Ya kara da cewa matasan sun musanta cewa auren jinsi suke daurawa, shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar dayansu suke yi.

Shugaban hukumar ya ce wadanda aka kama din suna tsare a hannun hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: