Akalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zabtarerwar kasa a Brazil

0 64

Akalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da kuma zabtarerwar kasa a Brazil bayan an shafe tsawon lokaci ana kwarara ruwan sama kamar da bakin-kwarya.

Lamarin ya auku ne a birnin Petropolis mai cike da wuraren kayatarwa da yawon bude ido kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Bayanai na cewa, akwai yiwuwar samun karin mamata, ganin yadda alkalumansu ke ci gaba da karuwa sannu a hankali, a daidai lokacin da masu aikin ceto ke ta kokarin nemo masu sauran numfashi.

Dimbin mutane ne dai ke ci gaba da makalewa a cikin laka da kuma tarin buraguzai.

Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Talatar nan.

Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: