Babban jami’in lafiya da ke bai wa shugaban Amurka Joe Biden shawara kan cutar korona, Dr Anthony Fauci, ya ce lokaci ya yi da Amurkawa za su fara komawa gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Dr Fauci ya ce duk da cewa har yanzu cutar nan ba ta yi ƙaura ba, amma babu yadda za a ci gaba da rayuwa a haka.

Wanna dai na zuwane daidai lokacin da hakumomi a kasar ke sanar da shirin kirkiro sabbin matakan kariya ga cutar.

Hakumomi a jihohin new jersey, New York, California, Connecticut, Delaware da Oregon sun bayyana shirnin su na tsagaita dokar sanya takunkumi a makarantu da sauran gurare nan da yan makonni.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake samun raguwar masu kamuwa da cutar nau’in Omicron, da kuma raguwar masu mutuwa da kusan 2,200 a kowace rana, wanda yawancinsu basu karbi riga kafin cutar ba.

Kimanin mutane dubu 147 ne suka kamu da cutar a wannan makon a kasar.

Haka kuma mutane dubu 9,500 ne ke zuwa asibitoci daban-daban a kowace rana a fadin kasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: