

- Yadda yan IPOB suka kashe ‘yan Arewa 10 ciki har da mace mai juna biyu da ‘ya’yanta 4 da wasu mutane 6 a jihar Anambra - May 24, 2022
- Sama da mutane 30 ne aka ruwaito sun bace a jihar Borno bayan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai musu hari - May 24, 2022
- Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya karbi tikitin takarar Sanatan Gombe ta Arewa domin tsayawa takara a jam’iyyar PDP a 2023 - May 24, 2022
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matsalar yawan Yaran da basa zuwa Makaranta ba kawai a Arewacin Najeriya ta tsaya ba, matsala ce da ta shafi kasar baki daya.
Da yake Jawabi a taron Ma’aikatar Ayyukan Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma, Shugaban Lura da Shirin Yaki da Talauci na kasa Dr Umar Buba Bindir, ya ce a yankin Makoko da ke Jihar Lagos kadai Kimanin Yara dubu 7,000 ne basa zuwa Makaranta.
A cewarsa, haka lamarin ya ke a Jihar Enugu da ke Kudancin Kasar nan da kuma birnin Jos na Jihar Fulato.
A Jawabinta, Ministar Ma’aikatar Jinkai Iftila’i da Cigaban Al’umma Sadiya Umar Farouk, ta ce Kimanin Yara Miliyan 10 basa zuwa Makaranta a Najeriya.
Haka kuma ta ce a yanzu haka akwai Kimanin mutane Miliyan 46 a Rijistar Ma’aikatar.
Ministar ta ce shirin bada tallafin Naira dubu 5,000 ga masu karamin karfi, ya tallafawa yan Najeriya da dama wajen fita daga Talauci.
Kazalika, ta ce gwamnatin tarayya tana yunkurin kirkirar wani shiri domin tallafawa Matasa dubu 300 wanda suka kammala aikin Npower, inda zata hada su da Bankin CBN domin basu bashi.