Ministar Agaji da Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar Farouq, ta ce tunanin ’yan boko ne ke cewa N5,000 da Gwamnatin Tarayya take ba wa talakawa a wata-wata ta yi kadan ta fitar da su daga talauci.

Sadiya ta bayyana haka ne bayan an yi mata tambaya game da amfanin da N5,000 da gwamnati ke ba wa talakawa a duk wata a yunkurinta na fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

A cewarta, ma’aikatar da take jagoranta ganau ce kan yadda N5,000 din da ake biyan talakawa masu rauni a wata-wata ke taimakawa wajen fitar da su daga matsanancin talauci.

Hajiya Sadiya ta ce idan aka lura, mutanen da aka ba wa N5,000 din tana da matukar muhimmacni a gare su, domin talakawa ne masu rauni, kuma tana kyautata musu rayuwa.

Sadiya ta yi wannan bayani ne a jiya yayin yawabin mako-mako da Fadar Shugaban Kasa ta shirya.

Sai dai ta bayyana cewa amma akwai wasu ’yan Najeriya da N5,000 din ba ta kai yawan kudin katin da suke sanyawa a wayoyinsu ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: