Rundunar yansandan jihar Jigawa ta kama wani mutum a karamar hukumar Babura bisa da kashe yar sa

0 94

Rundunar Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum mai suna Hannafi Yakubu dan shekara 40 a kyauyen Achiya na karamar hukumar Babura bisa zargin sa da kashe yar sa mai suna Salima Hannafi yar shekara 11 biyo bayan dukan ta.

Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Dutse, inda ya ce lamarin ya faru ne a Karamar hukumar Babura.

Sanarwar ta ce Hannafi, ya kashe yar tasa ne ta hanyar Marin ta, inda ta fadi nan take.

ASP Lawan Shiisu Adam, ya ce a ranar 12 ga watan Fabreru ne suka samu labarin daga kyauyen Achiya na karamar hukumar Babura cewa wani mutum mai suna Hannafi Yakubu, ya mari yarsa Salima mai shekara 11 da hannu, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar ta.

Kakakin yan sandan ya ce biyo bayan faruwar lamarin ne suka dauki yarinyar zuwa Asibitin Kwantarwa na Babura domin tabbatarwa, inda Likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Kazalika, ya ce an dauki hoton wurin da Mahaifin nata ya Mareta, kafin a yi mata Jana’iza kamar yadda Addinin musulunci ya tana da, kuma ana cigaba da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: