Jihar Jigawa ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan saukaka hanyoyin gudanar da kasuwanci

0 92

Jihar jigawa ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan saukaka hanyoyin gudanar da kasuwanci wanda ya samu halartar masu kanana da matsakaita da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Babban mai masaukin baki kuma gwamnan jihar jigawa Muhammad Badaru Abubakar yace Shirin ya samu gagarumar cigaba ga gwamnati da kuma yan kasuwa a jihar nan

Shirin samarda hanyoyin kasuwanci cikin sauki, tsarine da gwamnatin tarayya ta bullo dashi karkashin majalisar kula da tattalin arziki ta kasa a ofishin mataimakin shugaban kasa domin nemo hanyoyin tallafawa yan kasuwa na gida da kuma na ketare dake da sha’awar zuba jari a Najeriya.

Gwamna Badaru Abubakar yace a kokarin da ake na magance wasu daga cikin matsalolin dake addabar yan kasuwa tuni gwamnatin tarayya ta amince akafa karin tashoshin samarda wutar lantarki guda hudu afadin jihar.

Itama mai bawa shugaban kasa shawara kan shirin saukaka yin kasuwanci Dr Jumouka Oduwale tace tawagarta ta dade tana bibiyar manufofi da tsare-tsaren jihar jigawa kan shirin, don batayi mamakin yadda jihar ta kasance a mataki na uku ba a jerin jihohi da sukafi yin saukin kasuwanci a Najeriya.

Haka zalika wasu daga cikin yan kasuwar da shirin ya tallafawa cigaban sanaoinsu sun tofa albarkacin bakinsu.

Taron yasami halartar wakilin majalisar zartarwa na jiha dana kananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: