Hukumar JAMB ta bankaɗo daliba 3,000 na bogi da suka kammala karatun jami’a

0 113

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta ƙasa (JAMB) ta bankaɗo daliban da suka kammala karatun jami’a na bogi 3,000 da kuma mallakar takardun shaidar kammala karatu ba bisa ƙa’ida ba a faɗin ƙasar.

Magatakardar hukumar, farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan, kuma ya ce waɗannan mutane ba su taɓa zuwa jami’a ba, wanda hakan ya nuna irin cin hanci da rashawa da ake samu a harkar ilimi, yana mai cewa hakan abin kunya ne ga al’ummar ƙasar.

A watan Disamban 2023, Kwamitin Majalisar Wakilai kan Ilimin Farko ya buƙaci Hukumar JAMB ta samar da jerin sunayen cibiyoyin da ke da hannu wajen shigar da ɗaliban jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba. Oloyede ya lura cewa daga shekarar 2017 zuwa 2020, cibiyoyin karatu a fadin kasar nan sun shigar da sama da ɗalibai 706,000 jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: